27 Yuni 2021 - 14:02
​MDD:’Yan Ta’adda Sun Kashe Akalla Mutane 350,000 A Arewa Maso Gabacin Najeriya

Majalisar dinkin duniya ta bada rahoton cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta boko haram kadai ta kashe mutane 350,000 a arewa maso gabacin tarayyar Najeriya a cikin shekaru 10 da suka gabata, sannan wasu miliyon 8.7 suna bukatar taimakon gaggawa wadanda suka hada da abinci da wuraren zama.

ABNA24 : Rahoton ya kara da cewa miliyon 13.10 daga cikinsu su na zama ne a yankin da rikicin yake faruwa.

Jaridar Tribune ta Najeriya ta bayyana cewa wakilan MDD tare da na kasashen da suke bada tallafin, wadanda suka hada da Amurka sun tabbatar da cewa an kashe dala biliyon $1.45 a cikin shekaru 6 da suka gabata a kan ‘yan gudun hijira a yankin.

Jakadan Amurka a Najeriya , Ms Mary Beth Leonard wacce ta halarci taron ta godewa kungiyayoyin da suka aiwatar da shirin samar da tallafi ga wadanda abin ya shafa a yankin. Gwamnan jihar Boron Babagana Zulum wanda ya sami halattan taron ya bayyana cewa kungiyoyi da kuma kasashen da abin ya shafa kan cewa akwai bukatar a bunkasa bagaren tallafawa yan gudun hijira da kuma da kuma samar masu matsuguni .

342/