ABNA24 : Wata majiya wacce ta bukaci a sakaya ta ta shaida wa kafar watsa labaru ta Skynews Arabic cewa; An yi amfani da jiragen sama marasa matuki guda biyu ne wajen kai harin.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan asarar da harin ya haddasa.
A gefe an kai wani harin da makamai masu linzami akan sansanin soja na Victoria da ke kusa da Birnin Bagadaza. Majiyar sojan Amurka ta tabbatar da kai harin sai dai babu wata asara da ya haddasa kamar yadda ta amabta.
Da akwai sojojin Amurka da su ka kai 2000 a cikin dukkanin sansanonin sojan biyu da aka kai wa harin.
342/