ABNA24 : Buhari, ya kwatanta rasuwar babban hafsan sojojin a matsayin wani abu da zai haifar da koma baya ga kasar.
A wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, Buhari ya kuma yi addu’a ga mamatan, tare da cewa ba za a manta da irin saudakarwar da suka yi ba.
A watan Janairu, ne shugaba Buhari ya nada Janar Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.
Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgi da ya auku a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna a arewa maso yammacin kasar, tare da wasu mutum 10 da suka hada da manyan sojoji da kuma mambobin jirgin.
Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Kaduna a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, kuma ba’a kai ga bayyana musababin hatsarin jirgin ba.
Wannan shi ne karo na uku a wannan shekara da jirgin sojin Najeriya ke yin hatsari ko ya bata.
342/