ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya na cewa, rahoton kungiyar wacce take da cibiyar a birnin News York na kasar Amurka ya kunshi shafuka 213 kuma ta bayyana cewa za ta mika rahoton ga kotun hukunta man-manyan laifuffuka ta ICC.
Kenneth Roth babban darakatan kungiyar ta Human Right Wacht ya bayyana haka a safiyar yau a birnin NewYork, ya kuma kara da cewa yahudawan Isra’ila su na azabtar da Falasdinawa ba don kome ba sai don su falasdinawa ne, sannan suna fifita yahudawa kan falasdinwa don kawai su yahudawa ne.
Rahoton ya kammala da cewa yahudawan sun kori miliyoyin falasdinawa daga gidajensu.
A cikin watan da ya gabata ne, kotun ta ICC ta bada sanarwan cewa za ta fara bincike kan al-amuran take hakkin bil’adama a kasar haramtacciyar Isara’ila.
342/