ABNA24 : Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; A cikin kwanakin bayan nan, duniyar ta ga yadda sharrin da ‘yan sahayoniyar su ka bude ya zamar musu kaikayi koma kan mashekiya, don haka jamhuriyar musulunci ta Iran za ta mayar da martani mai karfin gaske akan duk wani gigin na ‘yan sahayoniya.
Kwanaki kadan da su ka gabata kafafen watsa labarun HKI sun ce an ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi a yankin “ Bi’iri-Saba’a” da kuma a tsakiyar Palasdinu da ke karkashin mamaya.
342/