ABNA24 : Jaridar Egypt Daily ta kasar Masar ta nakalto Al-Burhan yana fadar haka a wata hira da ta hada shi da tashar talabijin ta Al-Arabiyya a ranar jumma’an da ta gabata. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin Sudan tana bukatar Habasha ta janye sojojinta daga bangaren kasar Sudan da take mamaye da su.
Banda haka Al-Buryan yayi magana kan wasu al-amura da suka shafi kasarsa wadanda suka hada da rikicin madatsar ruwa ta Renaissance ta kasar Habasha da rikikin yankin Darfur da kuma matsalolin tattalin arziki wanda kasar take fama da su.
342/