ABNA24 : Dakta Qalibaf ya bayyana hakan a jawabin da yayi yayin bude taron makon hadin kan al’ummar musulmi karo na 34 da aka gudanar a nan birnin Tehran inda ya ce: Cin zarafin Annabi (s.a.w.a) yana a matsayin cin zarafin dukkanin Annabawa da kuma saukakkun Littafa na Ubangiji ne. Duk wani mutum ko kuma wata cibiyar da ta aikata hakan kuwa toh ba ta san inda aka sa gaba ba.
A wani bangare na jawabin nasa, shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya tabo batun Falastinu a matsayin wani lamari wanda musulmi suka yi ittifaki kansa a matsayin wani hakki na al’ummar Falastinu, don haka sai ya ce; shugabannin kasashen da suka kulla alaka da HKI su san cewa wannan kawance na su ba zai jima ba, to amma abin kunya da bakin cikin hakan zai ci gaba da binsu tsawon tarihi.
A yau ne dai aka fara gudanar da bukukuwan makon hadin kan al’ummar musulmi don tunawa da ranar da aka haifi Fiyayyen halitta, Manzon Allah (s.a.w.a) kamar yadda marigayi Imam Khumaini, wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bukata kuma ya sanya wa wadannan ranakun ranakun makon hadin kai.
342/