20 Oktoba 2020 - 13:42
​Rauhani: Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Mataki Da Zai Hada Kan Al’ummar Afghanistan

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, kasarsa na goyon bayan duk wani mataki da zai taimakawa wajen samun hadin kan al’ummar kasar Afghanistan.

ABNA24 : Shugaba Rauhani ya ba yyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar sulhu ta kasar Afghanistan Abdullah Abdullah, wanda yake gudanar da ziyarar aiki a birnin Tehran.

Ya ce ko shakka babu, al’ummar kasar Afghanistan mutane ne masu himma da kwazo a dukkanin bangarori, saboda haka za su iya warware matsalolinsu da kansu, ba tare da wasu kasashe sun yi musu katsalandan ba, domin kuwa shigar kasashen ketare a cikin lamurran kasar ne ya kara dagula komai a cikin kasar ta Afghanistan.

Shugaba Rauhani ya ce; kasantuwar Afghanistan kasa ce makwabciya ga Iran, baya ga haka kuma abubuwa da dama sun hada al’ummomin kasashen biyu, musamman addinin muslunci, wannan ya sanya Iran ba za ta taba yin watsi da bukatun al’ummar Afghanistan ba a duk lokacin da suke bukatar taimakonta.

Haka nan kuma ya yi ishara da aikin gina layin dogo da ake a ladin Harat na Afghansiatan wanda zai hada kasar da kasar Iran, inda shugaba Rauhani ya ce Iran din za ta kammala wannan aiki nan ba da jimawa ba, kuma al’ummomin kasashen biyu za su fara cin gajiyar hakan nan da ‘yan lokutan kadan masu zuwa.

342/