ABNA24 : Isma’ila Haniyyah ya ci gaba da cewa; Daukar fansa da za mu yi akan abokan gabar da su ka aikata kisan kiyashi a Sabra da Shatila, shi ne korarsu daga kowane taku daya na kasar Palasdinu.”
Shugaban na kungiyar Hamas wanda ya halarci taron kungiyoyin Palasdinawa a Beirut, ya bayyana cewa; A wannan lokacin ana yin taron a Lebanon,amma anan gaba za a yi shi ne a birnin Qudus.”
Har ila yau Isma’ila Haniyyah ya ce; Ina jinjinawa gwagwarmayar Lebanon wacce ta turmusa hancin makiya a kasa a shekarun 2000 da kuma 2016.
342/