(ABNA24.com) Gargadin na hukumar lafiya ta duniya, yana zuwa ne adaidai lokacin da wadanda su ka kamu da cutar corona a fadin duniya yah aura miliyan 12
Shugaban hukumar lafiyar ta duniya Adhanom Ghebreyesus ya ce; cutar ta Covid-19 wacce kusan kowane mutum guda a duniyar nan ya tasirantu da ita, ta cancanci a sake yin nazari mai tsafta akan yadda ake fada da ita.
Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa; A kowace rana ta Allah cutar sai kara muni take yi, kuma ta fi karfin a shawo kanta a cikin yankuna mafi yawa na duniya.
Shugaban hukumar kiwon lafiyar ta duniya ya kara da cewa; Babu yadda za yi mu iya samun galaba akan cutar matukar kawukanmu suna ci gaba da rarraba, yana mai karawa da yin gargadin cewa; sabanin da ake da shi a tsakanin kasashe a duniya yana taimakawa wajen kara yaduwar cutar.
342/