15 Yuni 2020 - 09:02
An Kashe Dansanda Guda Da Sojoji Biyu A Kasar Kenya

Majiyar jami’an tsaro a kasar Kenya ta bayyana cewa an kashe jami’in dansanda guda da kuma sojoji biyu, a wata musayar wuta a yankin Mandera daga arewa maso gabacin kasar a jiya Lahadi

(ABNA24.com) Majiyar jami’an tsaro a kasar Kenya ta bayyana cewa an kashe jami’in dansanda guda da kuma sojoji biyu, a wata musayar wuta a yankin Mandera daga arewa maso gabacin kasar a jiya Lahadi

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar tana cewa an kashe jami’an tsaron ne a musayar wuta tare da ‘yan ta’adda wadanda suke kokarin lalata wasu kayakan sadarwa a a yankin da ke kan iyaka da kasar Somali.

Labarin ya kara da cewa an kashe ‘yan ta’adda biyu a musayar wutan, sai dai majiyar bata bayyan sunan kungiyar ‘yan ta’addan da aka yi musayar wutan da su ba.

Sai dai kungiyar ‘yan ta’adda ta Alshabab ta kasar Somalia ta saba kai iran wadan nan hare-hare a cikin kasar ta Kenya don matsa mata lamba ta janye sojojinta wadanda suke aikin a cikin rundunar kasashen Afirka a kasar ta Somalia.

Jeremiah Kosoim wani jami’in tsaro na kasar ta Kenya ya shaidawa reuters cewa wani yaro matashi ya ji rauni a lokacin musayar wutan.

Kasar Somalia dai tana cikin tashe-tashen hankula fiye da shekaru 20 da suka gabata.



/129