(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Hassan Rohani a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da fira ministan kasar Iraki Mustapha kazimi ya fadi cewa: yanci da zaman lafiya da tsaron kasar Iraki yana da muhummancin sosai, don haka Iran za ta ci gaba da tsayawa tare da alumma da gwamnatin kasar domin akwai manufofi ma su yawa da suka hadasu.
Ya ci gaba da cewa kamar yadda muka tabbatar da goyon bayanmu a yaki da yan kungiyar ta’adda ta Daesh da kasar ta Iraki ke yi, haka zalika zamu ci gaba da kasancewa tare da gwamnatin kasar wajen ganin ta dawo da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a kasar,
Daga karshe Rohani ya yi nuni game da muhimmancin kara kyautata dangantakar tattalin arziki da suka hada da kasuwanci tsakanin iyakokin kasar , da kuma aiki da yarjejeniyar da aka rattaba hannun tsakanin domin bunkasar tattalin arzikin kasashen, da suka shafi shinfida bututun mai da kammala shinfida layin dogo da zai hade yankin Shalamche, da kuma yashe tekun Arvand.
/129
12 Mayu 2020 - 07:57
Lambar labari: 1036010
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da fira ministan kasar Iraki Mustapha kazimi ya fadi cewa: yanci da zaman lafiya da tsaron kasar Iraki yana da muhummancin sosai, don haka Iran za ta ci gaba da tsayawa tare da alumma da gwamnatin kasar domin akwai manufofi ma su yawa da suka hadasu.