20 Afirilu 2020 - 06:32
Iran: An Kaddamar Da Sabbin Na’urori Biyu Na Hango Sararin Samaniya ( Radar)

Da safiyar yau Lahadi ne dai sojojin na Iran su ka kaddamar da sababbin na’urorin hango sararin samaniyar na Radar masu dauke da sunayen; Khalij-Fars da kuma Muraqib”, inda kwamandan sojan sama

(ABNA24.com)  Da safiyar yau Lahadi ne dai sojojin na Iran su ka kaddamar da sababbin na’urorin hango sararin samaniyar na Radar masu dauke da sunayen; Khalij-Fars da kuma Muraqib”, inda kwamandan sojan sama na Barikin Khatamul-Anbiya, Janar Abdurrahim Musawi ya sami halarta, haka nan kuma babban kwamandan rundunar sama na sojojin Iran kanar Ali Riza Sabahi Fard

Ita dai na’urar ta hango sararin samaniya samfurin “Muraqib” tana iya tsinkayo wani abu daga nisan kilo mita 400. Ita kuwa na’urar hango sararin samaniyar ta Khalij-Fars, tana iya tsinkayo wani abu da ha yada jiragen sama da nau’oinsu mabanbanta daga nisan kilo mita 800.


/129