16 Afirilu 2020 - 04:59
Najeriya: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Dokar Hana Fita Na Tsawon Mako Guda

Gwamnatin jihar Kano a arewacin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa za ta hana mutane fita daga gidajensu na tsawon mako guda daga karfe 10 na daren gobe Alhamis.

(ABNA24.com) Gwamnatin jihar Kano a arewacin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa za ta hana mutane fita daga gidajensu na tsawon mako guda daga karfe 10 na daren gobe Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran “Reuters” ya nakalto Abba Anwar kakakin gwamnan jihar yana fadar haka a jiya Talata. Anwar ya kuma kara da cewa za’a rufe dukkanin kasuwannin da kuma wuraren taruwar mutane a duk fadin jihar a cikin kwanaki 7 daga goben.

Labarin ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai an gano mutane 4 dauke da cutar a jihar ta Kano, sannan gwamnatin Jihar za ta bi sawun wadanda suka hadu da wadannan mutane 4 don tabbatar da cewa ba su yada cutar a cikin jihar ba.

Kafin haka dai gwamnatin tarayyar Kasar ta hana fita a jihohin Lagos da Ogun da kuma babban binin tarayyar Abuja.

Ya zuwa yau Laraba dai mutane 373 aka tabbatar da kamuwarsu da cutar ta Corona a Najeriya, inda mutane guda 11 daga cikinsu suka rasa rayukansu, a yayin da 99 kuma suka warke daga cutar.


/129