Majalisar Dokokin Yemen sun yi Allah-wadai da harin da jiragen yakin Saudiyya suka kai kan gidan yari a garin Al-Hazm na lardin Al-Jawf, suna kiran sa a matsayin cin zarafi na yaƙi a fili. A harin, fursunoni 14, ciki har da yaro da mace, sun yi shahada tare da jikkata.
Ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na lardin Sa'ada na Yemen ya bayyana cewa hare-haren Saudiya ya zuwa yanzu sun yi sanadin shahadar fararen hula 356 da raunata 2,632.
A yau Litinin Saudiyya ta kai hare-hare ta sama a kan Yemen, inda jiragen yakinta suka kai hari a filin jirgin sama na kasa da kasa na Sana'a, a wani sabon tashin hankali wanda, a cewar sojojin Yemen, ya kawo ƙarshen matakin sassauta musayar wuta.