Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

26 Mayu 2021

11:06:32
1144467

Putin Da Biden Zasuyi Ganawar Keke da Keke Ta Farko A Watan Yuni

Shugabannin kasashen Amurka da Rasha zasu gana a ranar 16 ga watan Yuni mai zuwa a Geneva, kamar yadda fadar shugaban kasar Amurka da ta Kremlin suka sanar.

ABNA24 : Idan hakan ta kasance ita ce ganawar keke da keke ta farko tsakanin shugabannin biyu, wato Vladimir Putin da kuma Joe Biden.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke zaman doya da man ja kan batutuwa da dama tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin Amurka ta Joe Biden.

Biden dai ya jima ya sha caccakar takwaransa na Rasha, amma ya ce yana fatan yin huldar da Rashar kan batutuwa da masu masu mahimmanci.

342/