-
Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Ga Munanan Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Tehran Dangane Da Ayyukan Sojin A Kasar Yemen.
A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana cewa, zarge-zargen da ba su da tushe balle makama da ake ci gaba da danganta mata na jarumtakar al'ummar kasar Yemen wajen kare kai da goyon bayan al'ummar Palastinu ga Iran wani cin fuska ne ga wannan al'umma da ake zalunta.
-
Fursunonin Gidan Yarin Hillah Na Lardin Babil Sun Tsere, Ana Ci Gaba Da Bincike A Kansu
Iraki ta bayar da sanarwar tserewar fursunoni daga gidan yarin Hillah na lardin Babil, tare nemansu ruwa a jallo
-
Aikin Hajji Manhaja Ce Ta Wayewar Musulunci, Kuma Hanya Ce Ta Tabbatar Da Al’umma Daya Dunkulalliya.
Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da yake jaddada fa’idar aikin Hajji da damarmakin da ke cikinsa, ya dauke ta a matsayin dandali ne na tabbatar da al’ummar musulmi, ya kuma yi kira da a zurfafa amfani da wannan aiki na gina wayewa daga manyan mutane, jami’ai, da mahajjata.
-
Dakarun Yaman Sun Sanar Da Fara Hana Jiragen Isra'ila Ta Shi A Ko Ina
Sojojin Yaman sun fitar da wata sanarwa inda suka sanar da cewa za su kai hare-hare akai-akai kan filayen saukar jiragen sama na Isra'ila tare da katangewa ta sama kan gwamnatin kasar da nufin tallafawa al'ummar Palastinu.
-
Fitattun Abubuwan Da Suka Faru A Kisan Kiyashin Da Isra'ila Ke Yi A Gaza A Rana Ta 577
Dakarun mamaya na Isra'ila na ci gaba da kisan kare dangi a zirin Gaza, bayan sun ci gaba kisansu tun kwanaki 49 da suka gabata da kuma kwanaki 577 da fara kai farmakin Guguwar Aqsa. Hakan ya biyo bayan sabawar da Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da goyon bayan da Amurka ke yi na siyasa da soji, a yayin da kasashen duniya suka yi shiru da kuma watsin da ba’a taba ganinsa a kasashen duniya ba.