Wakilan mu sun ruwaito cewa, dakarun mamaya sun kaddamar da hare-hare da dama, yayin da illar hana shigowar kayayyakin abinci ya karu tun farkon watan Maris din da ya gabata. Wannan ya ba da zazzafar yanayin yunwar da al'ummar Zirin Gaza ke fuskanta.
Sabbin Abubuwan Da Suka Faru Daga Jiya Zuwa Yau
Tun daga wayewar garin Lahadi mutane 19 ne suka yi shahada. Sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na zirin Gaza.
Mutum daya ya yi shahada, wasu kuma sun jikkata, a yayin da jiragen yakin Isra'ila suka kai hari a gabashin Jabalia, da ke arewacin zirin Gaza.
Da sanyin safiyar yau ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar da wasu samame a garin Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza.
Hukumar tsaron farar hula ta sanar da cewa, an samu nasarar fitar da shahidai 15 sannan wasu 10 kuma suka samu raunuka bayan da jiragen Isra'ila suka kai hari kan ginin "Ramuz" da ke kusa da mahadar Al-Karamah da ke arewa maso yammacin birnin Gaza.
Wani sabon kisan kiyashi da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a yankunan Al-Karama da Al-Sultan a arewa maso yammacin birnin Gaza, ya yi sanadin mutuwar fararen hula 20, da jikkatar wasu, da kuma ci gaba da kasancewar wadanda suka bace a karkashin baraguzan gine-gine, yawancinsu mata da kananan yara.
Hukumar tsaron farar hula ta sanar da cewa, an samu nasarar fito da shahidai hudu, biyar da suka samu raunuka, sannan wasu da dama da suka bata na ci gaba da zama a karkashin baraguzan ginin, bayan da jiragen yakin Isra'ila suka kai hari gidan iyalan Al-Attar da ke yankin Al-Sultan da ke yammacin birnin Beit Lahia a arewacin zirin Gaza.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun tarwatsa wasu gine-gine a birnin Rafah, yayin da wasu makaman roka na Isra'ila suka yi luguden wuta kan yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza.
Wasu ‘yan kasar sun jikkata lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a wani gida a unguwar Al-Sultan da ke Beit Lahia a arewacin zirin Gaza.
Wani matashi Ahmed Al-Bayram ya yi shahada ne sakamakon raunukan da ya samu kwanaki biyu da suka gabata a lokacin da aka kai wa gidansa hari a yankin Al-Hawouz na Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.
Jiragen saman mamaya sun kaddamar da hare-hare biyu a arewa maso yammacin birnin Gaza, yayin da sojojin mamaya suka tarwatsa wasu gidajen jama'a a gabashin birnin Gaza.
Your Comment