29 Disamba 2019 - 07:15
Yemen : Kungiyoyi Sun Zargi Saudiyya Da kashe Fararen Hula

Kungiyoyi masu zaman kansu sun zargi kawancen Saudiyya da kashe fararen hula 17 A birnin Saada.

(ABNA24.com) Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan harin da aka kai kan wata kasuwa a birnin na Sadda inda fararen hula 17 suka rasa rayukansu, wanda kungiyoyin masu zaman kansu suka bayyana cewa babu makawa kawacen da Saudiyya ke jagoranci ne ya kai shi.

Harin dai shi ne irinsa na uku da aka kai a cikin wata guda a wannan yankin dake arewacin kasar ta Yemen.

Da yake bayyana halin da ake ciki a Saada, shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta Mwatana, ya ce halin da ake ciki ya jefa fararen hula a cikin halin ni ‘yasu.

Wasu alkalumma da MDD, ta fitar sun nuna cewa fararen hula, 89 ne aka kashe ko aka jikkata a hare hare da aka kai kan kasuwar ta Saada a cikin watan Nuwamba da ya gabata.

Tun dai bayan da Saudiyya ta shelanta yakin ba gaira ba dalili kan kasar ta Yemen a cikin shekara 2015, dubun dubatar mutane suka rasa rayukansu, kana wasu miliyan 3,3 suka kauracewa muhallensu, sai kuma wasu miliyan 24,1 dake bukatar tallafi a kasar.

MDD ta bayyana halin da ake ciki a Yemen a matsayin mafi muni a duniya.





/129