24 Nuwamba 2019 - 04:54
Iran Ta Kai Karar BBC A Hukumar Sadarwa Ta (Ofcom)

Ofishin jekadancin Iran, a birnin Landan, ya kai karar wasu gidajen talabijin dake wasa shirye shiryensu da harshen farisanci daga ketare a gaban hukumar sadarwa ta Birtaniya (Ofcom),

(ABNA24.com) Ofishin jekadancin Iran, a birnin Landan, ya kai karar wasu gidajen talabijin dake wasa shirye shiryensu da harshen farisanci daga ketare a gaban hukumar sadarwa ta Birtaniya (Ofcom), saboda nuna bangaranci da fifita wani bangare a lokacin zanga zangar baya bayan nan ta wasu jama’ar Iran kan nuna bacin rai game da kara farashin man fetur.

Kafofin yada labaren talabijin din sun hada da BBC-farsi a sahun gaba, da muryar Amurka (VOA), da ‘’Manato’’ da kuma ‘’Iran International’’, wadanda mahukuntan na Iran ke zargi da rura wutar zanga zangar lumanar data biyo bayan kara farashin man fetur a kasar ta Iran.

Jakadan Iran A Landan, Hamid Baïdi Nejad, ya ce wasikar da ya aike ta neman doka ta hau kan wadanan gidajen talabijin masu kin jinin Iran, wadanda sukayi amfani da damar kara farashin mai da gwamnatin Iran ta yi, domin wuce gona da iri da kuma nuna goyan baya ga bata garin da sukayi amfani da zanga zangar domin tada hargitsi.

A cikin wani sako kuma da aike a shafinsa na twitter, Mista Baïdi, ya ce al’ummar Iran ba zasu taba mantawa ba da irin wannan lokaci ba da wadanan tashohin a sahun gaba « BBC Persan », wadanda ke samun talafi daga gwamnatocin kasashen waje da magabatan waccen lokacin, ke matsa kaimi wajen ganin bata garin sun lalata dukiyoyin jama’a da kuma neman tada hankalin jama’a a kasar ta Iran.



/129