5 Oktoba 2019 - 04:39
Dr Iran Ali Larijani: Iran A Shirye Take Ta Tunkari Duk Wata Barazana Amma Kofofinta Abude Suke.

A wata tattaunawa da yayi da gidan talbijin din Aljazeera shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa, zai yi wuya wani yaki ya afku a yankin,...

(ABNA24.com) A wata tattaunawa da yayi da gidan talbijin din Aljazeera shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa, zai yi wuya wani yaki ya afku a yankin, Kuma Iran a shirye take domin tunkarar duk abin da ka iya faruwa , sai dai yana mai jaddada cewa kofofinta a bude suke a ko da yaushe don tattaunawa da kasar Saudiyya domin warware matsalolin da suke da sabani akai.

Da yake amsa tambaya game da tayin yarima mai jiran gado na kasar Saudiya bin Salman domin tattaunawa da Iran ya fadi cewa wannan lamari ne mai kyau, inda daga karshe saudiya ta farga cewa ta hanyar tattanawa ce kawai zaa iya warware rikicin yanki, ba dogaro da Amurka da ta yi ba, kuma bn salman ne zai bayyana yadda zaa warware rikicin ta hanyar siyasa da yace yafi fifitawa maimakon yaki da iran.

Ya kara da cewa kowa a yankin yayi imani cewa amfani da karfin soji ba zai warware matsalaba zai kara zafafa rikici ne, don haka iran ta yi amanna da kulla kyakykawar alaka siyasa da tattalin arziki da dukkan kasashen musulmi kuma kofofi a bude suke ga kowacce kasar musulmi ba tare da gindaya wani sharadi ba.




/129