(ABNA24.com) Ministan harakokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce shawarar da kasar Finland ta gabatar a baya na tattaunawa kan yankin tekun Fasha ta yi kama da wadda kasar Iran ta gabatar.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya ruwaito ministan harakokin wajen Iran Muhammad jawad Zarif yayin da yake tattaunawa da 'yan jaridu a birinin Helsinki fadar mulkin kasar Finland yana cewa a shekarun baya na ziyarci birnin Helsinki, kuma mun tattauna tare da hukumomin wannan birni, shawarar da suka gabatar kan yankin tekun fasha ita ce kafa wata tawaga ta tuntubar juna a yankin, shawarar da kasar Iran ma ta gabatar ta yi kama da wannan.
Zarif ya yi ishara kan irin muhimmancin da kasashen Finland da Sweden da Norway suka bayar kan batun yankin, inda ya ce kasar Sweden ita ce ta dauki nauyin shiryar zaman farko kan batun rikicin kasar Yemen, sannan kuma kasar Norway na kokarin shirya taro kan kasar Afganistan.
Yayin da yake tattaunawa da hukumomin kasar Finland, ministan harakokin wajen Iran ya ce dole ne a dama da kasashen Sweden da Norway wajen magance rikicin yankin, a yau yanayin da yankin yamacin Asiya ke ciki, musamman kasar Iran, akwai bukatar tattaunawa.
Har ila yau Zarif ya bayyana muhimmancin alaka da ke tsakaninsu, inda ya ce wajibi ne kasashen Turai su zartar da yarjejeniyar da suka cimmawa tare da kasar Iran kan shirinta na nukiliya a shekarar 2015.
A daren jiya Asabar ne ministan harakokin wajen Iran ya jagoranci tawagar kasar zuwa kasar Finland da nufin ganawa da hukumomin kasar.
Bayan kasar Finland, tawagar ta Zarif za ta ziyarci kasashen Sweden da Norway.
/129
19 Agusta 2019 - 07:05
News ID: 969951

Ministan harakokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce shawarar da kasar Finland ta gabatar a baya na tattaunawa kan yankin tekun Fasha ta yi kama da wadda kasar Iran ta gabatar.