(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin arabi 21 cewa, Ilham Omar ta rubuta wata makala wadda jaridar New York Times ta buga, a cikin makalar tana cewa, sau da yawa mutanen gari su ne suke yaudaruwa da kalaman nuna wariya ko kyamar wani jinsia cikin jama’a.
Ta ce haka lamarin yake a duk lokacin da aka samu bullar masu irin wannan tunani ba kasafai ake samun masana suna yaudaruwa da hakan ba, kamar yadda ko a Amurka ma ‘yan kasa na gari da suka san kimar kasarsu, ba sa cin zarafi ko nuna kyama ga wani saboda banbancin fahimta ko addini ko launin fata.
Ilham Imar ta ce abin da ya fi muni shi ne, yadda kasa kamar Amurka shugabanta ne yake da irin wannan akida, ta nuna kyama da wariya ga wani jinsi, saboda dalilai na bangaranci ko dai na launin fata ko addini ko kuma asalin da ba na Amurka ba.
Ta ce dole ne Amurkawa su mike domin kare kasasu daga gurbacewar tunani, tare da hana yaduwar irin wanann akida ta Trump a tsakanin al’ummar Amurka.
/129