1 Janairu 2019 - 16:24
Nageria: Buhari Ya Yi Alkawarin Gudanar Da Zabuka Cikin Gaskiya

A jawabinsa na shiga Sabuwar Shekara, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya jaddada alkawari da kudurinsa na yin babban zaben kasar cikin gaskiya da adalci.

Buhari ya bayyana 2019 a matsayin muhimmiyar shekara cikin tarihin kasar, ya ce lokacin shiga kowacce shekara, akan yi amfani da wannan dama wajen yin waiwayen baya da kuma saita alkiblar gaba.

A bana ne dai, Najeriya za ta gudanar da babban zaben shugaban kasar da gwamnoni da kuma 'yan majalisu.

"2019 za ta kasance shekarar zabe a gare mu. Nan da wata biyu za a yi zabuka, inda za mu zabi shugabanni kan matakai daban-daban a kasa da kuma jihohi," in ji shi

A cewarsa, babu bukatar zabuka su kasance wani al'amari na ko a mutu ko a yi rai ba, kuma bai kamata al'ummar kasar su tunkari wannan al'amari cikin tsoro da fargabar mutuwa ba.

Ya ce: "Abin farin ciki shi ne adadin mafi yawa na 'yan takarar shugaban kasar sun bayyana kudurin wajen tabbatar da zaman lafiya, zaman lafiyar da kuma za mu same shi."

Shugaba Buhari ya ce ketowar Sabuwar Shekara, wani lokaci ne da mayar da hankali gaba. A fuskanci sabbin al'amuran da za su zo, a shimfida tsare-tsare da shiryawa muhimman ranaku da harkokin da ke tafe.

"Wadanda ke ci gaba da yayata karairayi da sharrance-sharrance, don kansu, suna shure-shure ne kawai da ba zai hana mutuwa ba.

Mafi yawancin 'yan Najeriya sun amince kuma suna da yakinin cewa za mu cika alkawurranmu na tabbatar da dama ta baidaya ga kowa a zabuka, kuma abin da za mu yi ke nan," in ji Buhari.

Ya ce al'ummar Najeriya na muradin zaman lafiya da tsaro da karuwar arziki da samun damar shiga a dama da su da bunkasa ababen more rayuwa, a kasar da za yi alfahari da ita, a kasar da za ta iya tsare kanta a tsakanin kasashe.

Buhari ya kuma ce ya kuduri gina wata kasa da za a alkinta dukiyar da Allah ya hore mata wajen cin moriya mafi yawan 'yan Najeriya amma ba a rabe tsakanin wasu 'yan tsirarun masu uwa-a-murhu da zalamar biyan bukatun kansu ba ta karewa.

"A kan wannan tafiya muke gaba daya, ina kuma ba ku tabbacin tsayayyen kuduri kan akidun samun wata kasa amintacciya da ke da tsaro da adalci da tabbatar da raba-daidai da karuwar arziki.

Muna da kalubalanmu: tsaro da tattalin arziki da siyasa da zamantakewa, amma mun kuduri aniyar yaki da yin galaba kan dukkaninsu," in ji Buhari.