“ Kalmar ibada da dukkan ishtiqaqaat dinta anyi amfani da ita ne a cikin AlKur’ani da kuma a cikin dukkan hadisai da ma’anar ita kalmar da urf ta yau da kullum ta al’ada ta lugah. Wannan kuma dukkan kalmomin lugan larabci haka Alkur’ani yayi amfani dasu, haka nassosi na addini suka yi amfani dasu, ka da ka kebance da wannan, daga baya ne ake samo istilahi daga wa’yannan ma’anoni na urf da lugah. Saboda haka bai kebanta da kalmar ibada ba, yanda balarabe ya fahimci ma’anar ibada haka Alkur’ani yayi amfani da kalmar ibada, haka kuma hadisai.
“ Wato kenan, ibada ta musulunci akan wannan asasin shine tsayawa, shine aikata abinda za a iya ce mashi mika wuya gabaki dayanshi ya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala ta hanyar fuskantar da tafiyar da rayuwa a kan asasin umurnin Allah da kuma yardar da Allah. Da wannan ma’anar. Wato kenan, ba wai wani abu daya, biyu, uku, kaman yanda aka istilahantar a kai a yau shine ibada ba a mahangar Alkur’ani. Mika wuya gaba daya ya zuwa ga Allah Suhbanahu wa Ta’ala da wannan ake nufin ibada a cikin Alkur’ani da hadisai gabaki daya. Kuma domin shi Allah ya halicci dan Adam WAMA KALAKHTUL JINNA WAL INSA ILLA LIYA’ABUDUN, kuma ban halicci aljani da mutum ba sai domin su bauta min, wato rayuwarsu gabaki daya. Kuma dukkan Annabawa an aike su ne su je su fadawa mutane U’UBUDULLAHA, wato ku bautawa Allah. Sannan Subhanahu wa Ta’ala ya fuskantar da kidabi ya zuwa ga ‘yan Adam yace masu U’UBUDU RABBAKUM, ku bautawa Ubangijinku. Da wannan ma’anar ne aka yi amfani da Kalmar ibada a cikin nassosi na addini.
“ Mun gani Al-Imam AlKazim (as) wata rana yana wucewa a gidan daya daga cikin mabarnata masu almubazziranci da kece raini da dukiya, yana cikin gayan wannan jin dadi da facaka da dukiyan, ya zo wucewa ta gaban gidan Kaman yanda kuka sani sai ya ga wata kuyanga ta wannan mutumin ta zo tana so ta zubar da abincin da aka ci aka rage, zata zubar saura ko ragowa. To, sai ya tambaye ta dangane da mai gidan yace ‘shi da ne ko bawa’? To, lokacin da ita wannan kuyangar take mamaki take amsa AlKazim (as) alhali bata sanshi ba sai tace mashi ‘da’ ne mana. To, a lokacin sai AlKazim (as) yayi amfani da wannan Kalmar ta ibada da wannan ma’anar da muka fadi, sai yake ce mata LAU KANA ABDAN LA KAFA MIN MAULAHU. Yace mata kinyi gaskiya dan da ya kasance bawa to da ya ji tsoron Ubangijinshi. Abinda kawai yace mata Kenan kuma bata taba jin irin wannan maganar ba, sai ta ruga da gudu ta kuma cikin gida ta fadawa maigidanta din, to, shine ya fito da gudu yana so ya ga wane ne ya fadi wannan Kalmar. Labari mai tsawo, daga karshe dai ya zama Arifi, shi ake mashi Bishirul Arif.
“ Wato da kasance bawa da ya ji tsoron Ubangijinshi. Wannan itace ma’anar ibada a nassosin na addini. Amma su Fuqaha- Allah Ya yarda da wayanda suke da rai a yanzu, Ya gafartawa wayanda suka gabata- su sun sanya su ayyuka muhimmai a wani kaso daban da ake ce mashi ibadu. In muka ce ibada yau muna nufin wayannan, abinda yake sunanshi mu’amala, aqd, iqa’at. Wannan istilahi ne wanda malamai suka kirkiro suka istilahantar suka rage da’irar Ibada daga yanda take a urf da a lugah da kuma yanda take a Alkur’ani. Suka istilahantar da wannan bangaren suka sanya mashi suna Ibadu, amma duk da haka su kansu malaman suna ganin cewa dan Adam zai iya mai da rayuwarshi gaba daya ta zama ibada. Malaman fiqhu a lokaci guda suna ganin cewa dan Adam zai iya mai da rayuwarshi gabaki daya ta zama ibada da ma’ana da suka istilahantar din.
“ Saboda menene ma’anar ibada? Ibada a wurinsu shine abinda aka yi shi domin neman yarda da kusanci zuwa ga Allah a yau a istilahi. Shi yasa ko a ta’arifin Azumi wanda yana daga cikin jerin abinda suke ce ma ibada din. To, ko ta’arifin Azumi suna cewa Azumi shine kamewa daga ababen da suke karya shi daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana da nufin qurba da niyyar kusanci a istilah. To, duk da haka da wannan ma’anar wanda rukunan wannan ta’arifin guda uku ne; kamewa, muddar zamanin, da niyya. To, duk da haka suna ganin cewa mutum zai iya mai da rayuwarshi gabaki daya ta zama haka, kuma ko me yake yi A’AMMU MIN AN YAKUNA ko Azumi ne ko kuma tuka mota Taxi a biya shi kudi dukkansu gabaki daya zai iya mai dasu su zama ibada da ma’anar cewa don Allah yake yi. Mutum zai iya fitowa da safe ya tuka Taxi a biya shi kudi ya zama cewa ya samu lada, ibada yake yi saboda ya mai dashi don Allah Azza wa Jal yana neman lada kuma zai iya zama akasin haka, wato yana samun kudi ne kawai.”
20 Mayu 2018 - 13:18
News ID: 894220

A zama na biyu na tafsirin Alkur’ani wanda Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yake gabatarwa a cikin wannan wata na Ramadan yayi tsokaci da bayani dangane da ma’anar Ibada. Malamin yace: