Shafin watsa labaran ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a jiya Asabar ya bayyana cewa: Ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya gabatar da bayani da a ciki ya jaddada cewa: Kasashen Rasha da Iran gami da kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon suna yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda ne a Siriya bisa bukatar gwamnatin kasar.
Lavrov ya kara da cewa: A halin yanzu haka akwai sojojin wasu kasashen ymmacin Turai da suke da'awar yaki da ta'addanci a Siriya karkashin kawancen Amurka, kuma da a ce da gaske suke yakin, da zuwa yanzu an kai ga murkushe manyan kungiyoyin ta'addanci ta Da'ish da na Jabhatun-Nusrah.288