Abdeslam na daya daga cikin mutanen da ake zargi sun kai munanan hare hare a Paris, kuma a yau Juma’a ya ki bude baki ya yi Magana a lokacin da ya ke fuskantar tambayoyi a gaban alkali a yau Juma’a.
Hukumomin Faransa sun so Abdelsam ya bude bakinsa domin tatsar bayanai musamman kan yadda suka kitsa kai harin 13 ga watan Nuwamba a Paris inda aka kashe mutane 130 tare da samun Karin haske ko akwai wasu yan ta’adda da ke shirin kaddamar da hare hare.
Sai dai lauyan da ke kare shi ya ce matashin mai shekaru 26 yana bukatar lokaci kafin ya fara Magana.
A watan maris ne aka cafke Abdaslam a birnin Brussels na Belgium kafin mika shi zuwa Faransa a ranar 27 ga Afrlu.