‘Yan Tawayen Ukraine sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar amma har yanzu ana ci gaba da kai hare hare a Yankin.
Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama yace zai sanya hannu kan sabbin takunkumin da kasar za ta dorawa kasar Rasha duk da ya ke bai amince da wasu daga cikinsu ba.
Kasar Rasha na fama da matsalar tattalin arziki sakamakon takunkumin da kasashen Yammacin duniya suka kakaba mata.ABNA