24 Yuli 2014 - 15:15
Mash'al: Babu Batun Dakatar Da Bude Wuta Har Sai An Warware Batun Killace Yankin Zirin Gaza

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa ba zasu taba amincewa da duk wani shirin dakatar da bude wuta tsakaninsu da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba matukar babu batun kawo karshe killace yankin Zirin Gaza

A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a jiya Laraba: Shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas Khalid Mash’al ya fayyace cewa; Dole ne kafin gabatar da butun kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kowane bangare ya gabatar da bukatunsa, sannan a samu daidaiton baki a tsakanin bangarorin, bayan nan sai a sanar da lokacin dakatar da bude wuta.

Mash’al ya kara da cewa; Palasdinawa ba su taba amincewa da duk wata shawarar dakatar da bude wuta tsakaninsu da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba matukar babu batun kawo karshen killace yankin Zirin Gaza. Har ila yau Khalid Mash’al ya zargi gwamnatin Amurka da hannu a ayyukan ta’addancin da gwamnatin h.k.Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar Palasdinu tare da gudanar da siyasar munafunci kan batun Palasdinawa.