14 Yuni 2014 - 08:31
Ayatullahi Imami Kashani Ya Jaddada Wajabcin Hadin Kan Al'ummar Iraki Wajen Fuskantar Ta'addanci

Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a babban birnin kasar Iran ya jaddada wajabcin samun hadin kan al’ummar Iraki wajen fuskantar hatsarin ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi da suka yunkuro domin mamaye kasar.

A hudubar sallar juma’arsa ta yau a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran; Ayatullahi Imami Kashani ya tabo irin makirce-makircen da makiya ke ci gaba da kitsawa kan kasashe musamman kasar Siriya yana mai cewa; Gwamnatin Siriya ta yi nasarar murkushe ‘yan ta’addan kungiyar Daular Musulunci a Iraki da Sham ta Da’ish da aka jibge a cikin kasarta, don haka a halin yanzu ‘yan ta’addan na Da’ish suka tsallaka zuwa cikin kasar Iraki da nufin wargaza ta.

Ayatullahi Kashani ya fayyace cewa; Gungun ‘yan ta’adda masu dauke da akidar kafirta musulmi suna tsallakawa cikin kasashe ne daga wannan kasa zuwa wancan da suna daban daban, a wani lokaci da sunan Al-Qa’ida ko Taliban ko kuma Da’ish. Sakamakon haka babban makamin da Irakawa zasu dauka wajen fuskantar wannan babbar masifa kuma annoba shi ne samun hadin kai a tsakaninsu tare da dogaro da Allah.ABNA