Waken Yabo Da Jinjinawa Iran Da Bakin Al-kanaweey
1 . Jallah sarki ya nufata
Yau ƙasa ta Iran a santa
Mussulunci mannufarta
Ta fito kowa ya ganta
Tafi rana gun fitarta.
2 . Rundunar Sahyu-Amurka
Har da a'arabun nifãƙa
Masu ɓarna can a Makka
Sun yi burin kar a farka
Ga shi yau su ne da kuka .
3 . Don Iran ta mangaresu
Ko ace ta tarwatsa su
Mun gani a cikin gidansu
Ba sukuni duk ƙasarsu
Don kwa sun gane kurensu.
4 . Ta riƙe mashiga ta Hurmuz
Tattalin maƙiyanta "Ƴamrūz"
Ko a ran idi na "Nairūz"
Ba wucewa ko da "Excuze"
Koko jirgi yayyi ƙurmuz .
5 . Sun zamo ɓera a rami
Don gudun ɓarnar makami
Babbakarsu yake da ƙaimi
Yau Iran ta rusa komi
Ta saka su suna ta zulmi.
6 . Su maƙota ƴan asara
Masu yin bautar nasara
Sun ziga kuma sun yi kora
Yau wutar ta bar maƙera
Ɗakunansu taje ta hura.
7 . Sun ƙware gun yaɗa gaba
Ga ta'addanci da zamba
Don buƙatarsu da riba
Ayyukansu suke ta girba
Don kwa yaso hakka Rabba.
8 . To Aduwallahi ɗai ne
Ba shi banbance mutane
Babu Shi'a ba Basunne
Ko mutum ma kafiri ne
In yaƙi su ba zai ga kyau ba.
9 . Mamaya ce manufarsu
Don su sace arziƙi su
In da ɗanyen mai kagansu
Sai kace mayu su ƙyasu
Ko ta yaya ne a bi su .
10 . Kan mutane ya fa waye
Da ake yin kan ta waye
Yanzu babu batun alaye
Ba batun yin ɓoye-ɓoye
Ƙwal daka ta doke maye.
11 . Ga ta can Lubnan mazaje
Sun hana su sakat da gwabje
Ga Yaman da Iraƙi lauje
Mai riƙar maƙiya da sun je
Gazza rãmin mai garaje.
12 . Rabbana daɗa ƙarfafarsu
Dan isar Manzonka ba su
Kariya don wanzuwar su
Kar ka bar maƙiya su kar su
Don Aliyu tsare ƙasarsu .
Khãdimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
20 / Shawwal / 1447H - 9 / 4 / 2026
Your Comment