20 Afirilu 2026 - 09:16
Source: ABNA24
Dubban Al’ummar Morocco Sun Yi Zanga-Zanga Don Nuna Goyon Bayansu Ga Falasdinu

Dubban 'yan Morocco sun shiga wata babbar zanga-zanga a babban birnin kasar a ranar Lahadi don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da hare-haren da gwamnatin Isr’ilaa ke kai wa al'ummar Falasdinu da kuma nuna goyon bayansu ga fursunonin Falasdinu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da zanga-zangar ne don mayar da martani ga kiran da kungiyar National Action Group domin Falasdinu, kuma mahalarta sun rera taken neman a kawo karshen daidaita dangantaka da "Isra'ila" da kuma yanke hulda da wannan gwamnatin gaba daya.

Masu zanga-zangar sun tashi daga dandalin Babul-Ahad da ke tsakiyar Rabat, kuma bayan sun yi tafiya ta hanyoyi daban-daban a fadin birnin, sun isa gaban majalisar dokoki da tashar jirgin kasa ta Rabatul-Madina. Lauyoyi, 'yan siyasa, kungiyoyin kwadago da dalibai masu fafutuka, tare da 'yan kasa daga yankuna daban-daban na kasar, sun halarci gangamin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha