12 Afirilu 2026 - 00:53
Source: ABNA24
Irgc: Duk Wani Ƙoƙarin Jiregen Yaƙi Na Ƙetare Mashigar Hurmuz Zai Haɗu Hari Mai Tsanani.

Sanarwa mai lamba 58 ta dakarun juyin juya halin Musulunci yazo da cewa; Duk wani ƙoƙarin jiragen ruwan jami'an soji na ketare mashigar Hormuz za tai maganinsa hari mai tsanani. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin ruwa na IRGC suna da cikakken iko sarrafaws a mashigar Hormuz kuma izinin wucewa zai samu ne kawai bisa ga wasu ƙa'idodi ana ba da izini ga jiragen ruwa na farar hula ne kawai. Sannan dakarun sun ƙaryata labarin da ke yawo na wucewar jiragen ruwa na Amurka ta mashigar ruwan kuma duk wani yunƙuri na ketarewar jiragen ruwa za a magance shi da cikakken hari mai tsanani.

Your Comment

You are replying to: .
captcha