Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Hizbullah ta fitar da wani faifan bidiyon yadda ta kai harin makamai masu linzami nau’in (M-302 / Kheibar-1 Syria) kan sansanin sojojin Isra'ila na Stella Maris da ke arewa maso yammacin Haifa. Kungiyar Hizbullah domin kare kasar Lebanon da al'ummarta, a matsayin mayar da martani ga ta'addancin da gwamnatin Sahayoniya ta yi a kauyukan kudancin Lebanon da kuma mayar da martani ga karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da makiya ta sanar da cewa ta sake kai hari a garin Kriat Shamona da sauran wasu garuruwan yahudawan sahyoniyawa da makami mai linzami da roka.
Kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa za a ci gaba da kai hare-haren har sai Isra'ila da Amurka sun dai na kai hare-haren kan kasar da al'ummar Lebanon. Wani mai magana da yawun sojojin Isra'ila duk da boyewar da suke na irin asarar da suka samu ya tabbatar da jikkata sojoji biyu na sojojin Isra'ila a arangama a kudancin Lebanon.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, mayakan gwagwarmayar Islama sun yi wa garin Avium na Sahayoniya ruwan makamai masu linzami a yau Asabar. Hizbullah ta kai hari kan wata tankar Isra'ila a yankin Al-Adisa da makami mai linzami da kuma wani jirgi maras matuki wanda ya abin harinsa kai tsaye. A wata sanarwar kuma, kungiyar ta sanar da cewa, ta kai hari kan taron dakarun Isra'ila da motocinsu a garin Kriyat Shimona da makamai masu linzami. Sannan ta kai hari kan tankar sojojin Isra'ila a yankin Saful-Hawa na Bint Jbeil tare da wani jirgin sama mara matuki k ya kai hari kai tsaye. Har yanzu kungiyar Hizbullah tana gudanar da ayyukankai hare-haren makamai masu linzami zuwa arewacin yankunan da aka mamaye.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, a wani aiki na 11 na yau, ta kai hari ga garin Avium na sahyoniyawa da makamai masu linzami da dama. Yayin da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kai hari kudancin Lebanon, Hizbullah ta ba da rahoton kai hari kan wurin taron sojin Sahayoniya a garin Shama tare da wani jirgin sama mara matuki tare da yin barna kai tsaye. A yayin aikin gwagwarmaya ta kai hari kan wasu gungun Sahyoniyawa da dama da tankunan yakinsu a kudancin kasar. Hizbullah ta kai ahri kan ababen more rayuwa na soji a garuruwan SAFD da Adumim, sansanin sojin Ya’ara, garuruwan Naharia, da garuruwan Shamunah, Al-Mutla, da Maskaf a arewacin yankunan da aka mamaye. Kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami guda 10 kan Kremil da ke Al-Jalil, a cewar majiyoyin labarai. Akwai kuma rahotannin wani makami mai linzami da ya afkawa wani sansanin soji a arewacin Falasdinu ba tare da wata ƙararrawa ba. Sanna a karshe tana kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da gwamnatin Sahayoniya ta ke kaiwa kan kudanci da gabashin Lebanon.
Your Comment