5 Faburairu 2026 - 21:53
Source: ABNA24
Iran: IRGC Ta Jiragen Safarar Mai Biyu A Tekun Fasha.

Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ta sanar da kwace jiragen ruwa biyu da ke safarar mai a cikin Tekun Fasha, a matsayin wani bangare na ayyukanta na yaki da fasa-kwauri.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Bayan sa ido da bin diddigi sosai rundunonin sojojin ruwa na IRGC sun kame jiragen ruwa biyu kusa da Tekun Fasha. An gano sama da lita miliyan daya na man fetur da aka son guduwa da shi ta haramtacciyar hanya a cikin jirgin.

An kama ma'aikatan jirgin guda goma sha biyar, dukkansu 'yan kasashen waje, aka mika su ga hukumomin shari'a da suka dace don gudanar da shari'a.

Iran: IRGC Ta Jiragen Safarar Mai Biyu A Tekun Fasha.

Bayani sun nuna cewa jiragen ruwa biyu suna aiki a cikin wata hanyar safarar mai da aka tsara a cikin 'yan watannin da suka gabata. An gano inda suke kuma an bi diddigin su ta hanyar leken asiri, sa ido, da ayyukan bincike da Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ta gudanar.

........

Your Comment

You are replying to: .
captcha