27 Janairu 2026 - 10:44
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kashe Ma'aikacin Talabijin Na Al-Manar

Hizbullah ta Lebanon ta sanar a jiya cewa Ali Nuraddin, ma'aikacin talabijin na Al-Manar, ya yi shahada a wani harin sama da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta Lebanon ta sanar a jiya cewa Ali Nuraddin, ma'aikacin talabijin na Al-Manar, ya yi shahada a wani harin sama da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon.

Wata sanarwa daga Hizbullah ta ce: Kisan Ali Nuraddin alama ce ta hatsarin ci gaba da kai hare-hare kan kafofin watsa labarai ta kowane fanni, a cikin tsarin ta'addanci.

Your Comment

You are replying to: .
captcha