23 Janairu 2026 - 17:45
Source: ABNA24
Jiragen Dakon Jiragen Saman Amurka USS Abraham Lincoln Sana Kan Hanya Zuwa Gabas ta Tsakiya

Jirgin Ruwan dakon jiragen saman Amurka USS Abraham Lincoln yana kan hanyarsa ta zuwa Gabas ta Tsakiya cikin kwanaki masu zuwa bayan ya ratsa ta Mashigin Malacca.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jirgin ruwan mau daukar jiragen saman Amurka USS Abraham Lincoln yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa Gabas ta Tsakiya kuma ana sa ran zai isa nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Jaridar Washington Post ta ruwaito, kamar yadda ta ambato jami'an sojojin ruwan Amurka, cewa jirgin saman yana cikin Tekun Indiya a halin yanzu kuma ana sa ran zai isa yankin a cikin kwanaki masu zuwa.

A cewar bayanan bin diddigin jiragen ruwa, jirgin ruwan Amurka, wanda aka ajiye a Tekun Kudancin China a cikin 'yan kwanakin nan, ya ratsa Mashigin Malacca a ranar Talata, wata hanyar ruwa mai mahimmanci wacce ta haɗa Tekun Kudancin China da Tekun Indiya.

Wani jami'in sojojin ruwan Amurka ya ce jirgin ruwan yana kan hanyarsa ta yamma, tare da rakiyar jiragen ruwa uku.

Wannan ci gaban ya zo ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan Iran.

Duk da cewa jami'an sojin ruwan Amurka da sauran hukumomin tsaro ba su tabbatar da cewa rundunar Jiragen ruwan ta nufaci Gabas ta Tsakiya ba ne, amma yanayin da take ciki da kuma matsayinta a Tekun Indiya ya nuna cewa kwanaki kadan ne kawai kafin ta isa yankin.

Amurka ta riga ta mayar da jiragenta daga Tekun Pacific zuwa Gabas ta Tsakiya, inda aka canja hanyar jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln zuwa Gabas ta Tsakiya a shekarar 2024.

................................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha