2 Janairu 2026 - 20:32
Source: ABNA24
Babban Hadafin Gwamnatin Amirul Muminin, Imam Ali (AS), Shi Ne Shiryar Da Mutane 

"Masu adawa da ilimi su ne waɗanda ke da kusurwar akida kawai ta hanyar bayyana ra'ayinsu da ilimi. wanda Imam ya magance su da gamsar da su hujjoji. Masu adawa ta hanyar zanga-zangar siyasa kuwa da su kayi adawa da qudurorin Imam, Imam yayi musu mu'amala da hankali da haƙuri da kau da kai. Amma masu adawa da tsaro su ne waɗanda ke barazana ga tsaron al'umma, wanda Imam ya yi musu mu'amala da gaske cikin tsanani". 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Farfesa Sayyid Mujtaba Noormufidi, farfesa a makarantar koyon addinin Qom kuma shugaban Cibiyar Bincike kan Shari'a ta Zamani, ya ce a wata hira da ABNA: "Lalle Dangantakar da take tsakanin 'yancin faɗar albarkacin baki da yadda ya kamata ayi suka da daukar mataki kan tsaron jama'a na ɗaya daga cikin muhimman lamurra a fannin shari'a ta siyasa kuma ana ɗaukarsu a matsayin muhimman ma'auni don auna sahihancin gwamnatoci har zuwa yau".

Rayuwar Imam Ali (AS) A Gwamnati, Ka'idar Siyasa Mai Muhimmanci 

Farfesa Noormufidi ya bayyana game da mahimmancin wannan batu: "Masu mulki da sarakuna a koyaushe suna fuskantar abokan hamayya, kuma babban tambaya ita ce ya Yakamata mu yi mu'amala da su?. A makarantar Ahlul Bayt (AS), wannan tambayar tana da matsayi na musamman kuma don amsata dole ne mu koma ga rayuwar Amirul Muminin, Ali (AS), domin rayuwarsa ba wai kawai rahoto ne na tarihi ba sai ta zamo ka'idar siyasa mai nuna hanya". Ya ƙara da cewa: "Amirul Muminin (AS) ya yi mu'amala da abokan hamayya daban-daban ta hanyoyi daban-daban; tun daga yin haƙuri da tattaunawa zuwa ɗaukar mataki mai tsauri don kiyaye adalci da tsarin Musulunci.

Ta Yaya Imam Ali (AS) Ya Yi Mu'amala Da Abokan Hamayyar Aiyasa?

Da yake magana game da matakai uku na masu adawa a gwamnatin Imam Ali (AS), wannan farfesa a makarantar hauza ya ce: "Masu adawa da ilimi su ne waɗanda ke da kusurwar akida kawai ta hanyar bayyana ra'ayinsu da ilimi. wanda Imam ya magance su da gamsar da su hujjoji. Masu adawa ta hanyar zanga-zangar siyasa kuwa da su kayi adawa da qudurorin Imam, Imam yayi musu mu'amala da hankali da haƙuri da kau da kai. Amma masu adawa da tsaro su ne waɗanda ke barazana ga tsaron al'umma, wanda Imam ya yi musu mu'amala da gaske cikin tsanani". 

Noormufidi ya ƙara da cewa: "Misali bayyananne na waɗannan matakai uku shine yadda Imam ya yi mu'amala da Khawarijiwa, wanda suka fara da adawa ta ilimi kuma daga ƙarshe ya haifar da fito na fito da makamai a Nahrawan".

Ka'idojin Da Ke Gudanar Siyasa Ta Amirul Muminin (SAW)

Da yake bayyana ƙa'idodin da ke jagorantar halayen siyasa na Amirul Muminin (SAW), ya ce: "Adalci, kiyaye tsarin Musulunci, girmama muradun jama'a, da mutuncin ɗan adam su ne ƙa'idodi huɗu na mulkin Alawiyya. Wanda Imam Ali (SAW) ya kiyaye mutuncin ɗan adam ko da a gaban maƙiya ne kuma bai taɓa kaucewa daga da'irar adalci ba" Noor Mufidi ya ci gaba da cewa: "A yau, gwamnatin Musulunci dole ne ta dogara da wannan tsari domin daidaita tsakanin 'yanci da tsaro da kuma hana sake afkuwar rikice-rikicen san rai".

Babban Hadafin Gwamnatin Amirul Muminin (SAW) Shi Ne Shiryar Da Mutane

Sayyid Mujtaba Noor Mufidi ya kammala da cewa: "Babban manufar gwamnatin Amirul Muminin (SAW) ita ce shiryar da mutane zuwa ga farin ciki da kusanci ga Allah, kuma wannan burin ya kamata ya bayyana a cikin dukkan halaye na siyasa, al'adu, da zamantakewa. "A yau, yayin da sabbin nau'ikan barazana da adawa suka bayyana, rayuwar Imam Ali (AS) na iya zama jagora mai amfani ga tsarin addini don sarrafa rikice-rikice wanda suke kiyaye tsaro da mutuncin ɗan adam".

Your Comment

You are replying to: .
captcha