21 Disamba 2025 - 19:59
Source: ABNA24
Manoman Girka Suna Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Biyan Hakkokinsu

Manoman Girka sun ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati a ranar Lahadi, sun taru da taraktocinsu a wurare masu mahimmanci a manyan hanyoyin kasar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Manoman a yankunan Kardista da Trikala sun ajiye taraktocinsu a kan babbar hanya a tsakiyar Girka kuma sun yanke shawara akan dakewa.

Manoman a sassa daban-daban na Girka sun kafa shingayen hanyoyi kuma sun kara tsananta wannan matakin yayin da zanga-zangar adawa da rashin biyan tallafi da hauhawar farashin samar da kayayyaki ta karu.

Manoman Girka suna kara tsananta zanga-zangarsu, suna neman a biya basussukan tallafi da cikakken diyya ga kayayyakin noma da dabbobi.

A Larsa, makiyaya sun shiga birnin kuma sun nuna rashin gamsuwarsu da manufofin siyasar gwamnati ta hanyar zubar da madara da kuma watsa alkama.

Ana sa ran za a kafa wasu shingayen a wannan makon, inda zanga-zangar ta bazu zuwa tashoshin jiragen ruwa da hanyoyin ketare iyaka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha