17 Disamba 2025 - 09:28
Source: ABNA24
MDD: Sama Da Mutane 100 Ne Suka Mutu A Harin Jiragen Sama Marasa Matuki A Kordofan Na Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa sama da fararen hula 100, ciki har da yara 43, sun mutu a hare-haren jiragen sama marasa matuki a Sudan tun daga ranar 04 Disamba 2025.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: babban kwamishinan kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa akalla fararen hula 104, ciki har da yara 43, sun mutu a hare-haren jiragen sama marasa matuki da dama a yankin Kordofan na Sudan tun daga ranar 04 Disamba 2025.

Babban kwamishinan kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, yana nuna damuwa game da karuwar rikicin, ya nuna fadan da ke tsakanin sojojin Sudan, Rundunar gaggawa da kuma Kungiyar 'Yantar da Jama'ar Sudan-Arewa a Kordofan; yanki wanda ya kunshi jihohi uku a tsakiya da kudancin Sudan.

Bai bayar da karin bayani game da wadanda suka kai harin jiragen sama ba, amma ya ce hare-haren sun shafi asibitoci, makarantar yara har ma da sansanin Majalisar Dinkin Duniya.

.........................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha