19 Oktoba 2025 - 08:23
Source: ABNA24
Jami'ar Mata Ta Al-Kafeel Ta Yi Bikin Yaye Daliban Da Suka Kammala Karatu A Najaf + Hotuna

Atbatul Abbasiyya ta shirya bikin yaye daliban jami'ar mata ta Al-Kafeel, inda aka yi bikin yaye dalibai daga 2023 zuwa 2025. A taron an gabatar da jawabai da fina-fina da wakoki dama bajakolin abubuwan ilimi.

Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBaiti: Ofishin Babban Jami’in Harkokin Mata na Haramin Abbas (A) ya kammala bikin yaye dalibai mata na Jami’ar Mata ta Al-Kafeel da ke Najaf Al-Ashraf, wanda ya kunshi shekarun karatu na 2023, 2024, da 2025.

Bikin wanda aka gudanar karkashin taken "Ilimi sako ne... Kuma cika alkawari tafiya ce," an nuna wani fim da sashen ilimi da al'adu na harami mai tsarki ya shirya mai taken “Mai Griman Da Ya Tsayar Bakin Ruwa, wanda ya ba da labarin fatawar Jihadil-Kifai da kuma rawar da babbar hukumar addini ta taka a nasarar da Iraki ta samu kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Taron ya kunshi jawabi daga ofishin babban jami’in kula da harkokin mata, wanda mataimakiyar darakta Malama Firdous Ali Hassoun ta gabatar. Ta bayyana cewa jami'ar Ummul-Baneen (amincin Allah ya tabbata a gare ta) tana matsayin wani tsari na musamman na ilimi wanda ya hada ingancin addini da ci gaban fasaha wanda ya ke baiwa mata damar zama masu magana akan shiriya da tunani na gaske a cikin al'umma.

Sheikh Ali Mohan daga sashin kula da harkokin addini ya gabatar da lacca akan muhimmancin ilimi da yada shi. Shirin ya kuma kunshi bangaren tambaya da amsa daga gasar "Dausayin Sani" da jawabai daga bakin wakilan dalibai Namarq Riad Hashem (Bangaren Da’awa) da Hanan Hussein Halil (ilimin kur'ani), da kuma karanto wakoki daga mawakiya Zeina Hassan Abbas. An kammala bikin ne da bayar da kyaututtuka ga gasar tare da raba takardun shaidar kammala karatu ga manyan dalibai da ma’aikatan da suka shirya gasar.

Jami'ar Ummul-Baneen (amincin Allah ya tabbata a gare ta) wata cibiya ce ta yanar gizo wacce ta sadaukar da kanta wajen bayar da ilimin addini da al'adu ga mata kyauta ta sassa na musamman kamar karatun Al-Qur'ani da kuma shirye-shiryen wa'azi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha