3 Yuli 2025 - 13:59
Source: ABNA24
Isra'ila: Dole Ne Mu Mamaye Dukkan Faɗin Gaza

Ministan tsaron cikin gida na gwamnatin yahudawan sahyoniya ya yi kira da a mamaye zirin Gaza gaba daya tare da yiwa mazauna wannan yankin hijirar tilas da kuma share kungiyar Hamas.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) -Abna- ya habarta cewa: ministan tsaron cikin gidan gwamnatin sahyoniyawan Itamar Ben-Guer ya yi kira da a mamaye yankin zirin Gaza baki daya, ya kuma yi nuni da cewa wata dama ce da ke zuwa sau daya kacal a rayuwa.

A cewar Al Jazeera, Itamar Ben-Guer a wata hira da gidan talabijin na Isra'ila ta 14 ya ce: "Har yanzu ina jin sautin farin cikin Hamas, bai kamata lamarin ya kawo har yanzu ba. Idan ba mu hambarar da Hamas ba, yaranmu za su sha wahala da azaba".

Ya kara da cewa: "Ina sa ran Smotrich ya goya min baya kuma za mu je wajen Netanyahu tare mu shaida masa cewa ba shi da hurumin yin watsi da hambarar da Hamas".

Ministan tsattsauran ra'ayi na sahyoniyawan ya ce: "Dole ne mu mamaye dukkanin Gaza tare da karfafa yin hijira daga can. Ya isa haka, wannan wata dama ce ta sau daya a rayuwa".

Ya ce: "Ba zan taba yarda a amince da wata yarjejeniya da ba ta dace ba, babban kuskure ne a kawo agaji a Gaza, idan muna son yin nasara a Gaza, dole ne mu ci gaba da karfin tuwo, ba za mu iya dakatar da yakin ba har sai mun yi nasara, kuma mun shafe kungiyar Hamas. Dole ne mu mamaye zirin Gaza gaba daya, tare da kwadaitar da mutane yin hijira".

Your Comment

You are replying to: .
captcha