15 Yuni 2025 - 00:23
Source: ABNA24
An Lalata Hare-Hare Guda  Biyu Na Isra’ila Kan Cibiyar Nokiliya A Lardin Bushehr.

Gwamnatin Sahayoniya ta Nufi bangare na 14 na Kudancin Pars da hare-haren amma basu ci nasara ba

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti ta kasa da kasa ABNA ya bayar da rahoton cewa: a ‘yan mintoci kadan da suka gabata, an kai hare-hare da kananan jiragen sama masu saukar ungulu a bangare na 14 na matatar mai ta Kangan da matatar iskar gas na Jam, wadanda ke da alaka da tankokin LPG a kudancin lardin Bushehr. Nan take aka shawo kan gobarar tare da hana fashewar wasu muhimman wurare.

An kuma kai wani hari da jirgi mara matuki a kan masana'antar mai na Kangan. An dai kai harin ne kan jirgin mara matuki da ya kai harin, amma an gano tarkacen sa da ke dauke da bama-bamai a masana’antar sarrafa sinadaran mai.

Majiyoyin yankin da kuma shaidun gani da ido sun ce wani na’urar tsuntsu ne mai kama da jirgi maras matuki ne ya kai harin.

Dakarun tsaro da na agaji suna samun nasarar tafiyar da lamarin kuma babu bukatar damuwa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha