14 Yuni 2025 - 14:02
Source: ABNA24
Fararen Hula 60 Yarana Kananan Yara 20 Ne Su Kai Shahada A Harin Isra’ila Ta Kai A Ginin Jamaran Da Ke Birnin Tehran

Fararen hula 60 da suka hada da kananan yara 20 ne aka kashe a harin da sahayoniya suka kai a ginin Jamaran da ke birnin Tehran

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: tashar talabijin ta kasar Iran ta bayar da rahoton cewa, an kashe fararen hula 60 a harin da yahudawan sahyuniya suka kai a daren jiya.

Tashar talabijin ta Iran ta bayar da rahoton cewa, dukkan wadanda aka kashen fararen hula ne da suka hada da kananan yara 20, tare da yin nuni da cewa, dakarun yahudawan sahyoniya sun kai hari a wani yanki da ke yankin Jamaran da ke gabashin babban birnin kasar Iran.

Tashar talabijin ta Iran ta kara da cewa har yanzu ana ci gaba da kwashe gawarwakin shahidan, kuma ana sa ran adadin zai karu. A jiya manyan yankuna na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun fuskanci mummunar wuce gona da iri daga bangaren sahyoniyawan mamaya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha