ABNA24 : Harin dai ya zo ne a lokacin da shugaban kasar Muhamamdu Buhari yake ziyara a mahaifarsa ta Daura da ke jihar ta katsina.
Har zuwa yanzu dai jami’an tsaro suna bincike domin gano adadin daliban da aka yi awon gaba da su.
Wannan harin na ‘yan bindiga yana daga cikin mafi muni da aka kai a wata makarantar kwana, tun bayan harin da aka kai a garurun Dapchi a 2018 da kuma na Chibok a 2014 a yankin arewa maso gabashin kasar.
342/