ABNA24 : Har ila yau jakadan na Iran ya kara da cewa wajibi ne kuma hukumar ta IAEA ta dau matsaya na rashin nuna son kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila wacce take ci gaba da yin karen tsaye ga dokokin hukumar da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi.
Yayin da yake magana kan irin hadin kan da Iran take ba wa hukumar kuwa, jakadan na Iran a MDD ya ce Iran ita kadai ta dauki kashi 22% na binciken da hukumar take gudanarwa yana mai cewa hatta a cikin wannan yanayi na Korona amma jami’an hukumar suna ci gaba da gudanar da bincike a cibiyoyin nukiliyan Iran.
A watan Augustan da ya gabata ne dai, a wata ziyara da babban daraktan hukumar ta IAEA, Rafael Grossi ya kawo ziyara nan Tehran inda suka cimma yarjejeniyar aiki tare tsakanin hukumar ta Iran.
342/