ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nasarallah yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake jawabi dangane da maulidin manzon Allah (s).
Sayyid Nasarallah ya kara da cewa musulmi basu dorawa addinin kirista ko annabi Isa (a) laifuffukan ayyukan ta’addanci wanda Amurka da kasashen yamma suka aikata a kasashen Iraki, Siriya da Afganistan.
Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya bayyana cewa ‘yencin fadin albarkacin baki a kasashen yamma ba gaskiya bane, don suna nuna fuska biyu a aiwatar da wannan ‘yencin, inda ba’a isa a karyara Holocso ba, wato tastuniyar kissan yahudawa a Jamus.
Amma suka bawa kansu damar cin mutuncin addinin musulunci da musulmi ko manzon addinin musulunci ta yadda suka ga dama, da sunan ‘yanci fadin albarkacin baki.
Daga karshe Sayyid Nasararl ya bukaci kasashen yamma su daika taimakawa yan ta’adda wadanda wadanda suke zubar da jinin mutane ba tare da wani laifi ba.
342/