Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti-{abna}-yau kwanaki goma sha tara Kenan da maluman shi’a a Pakistan suka shiga wani yajin cin abinci na sai baba ta gani, Hujjatul islam Raji Abbas Jafari shugaban kungiyar na daya daga cikin masu yajin cin abincin wanda a halin yanzu yake asibiti sakamakon yanayin da halin shi ya shiga.
Masu yajin cin abincin suna bukatar hukumomin kasar da su dubi yanayin zaluncin da ake yima yan shi’a a garin Islam Abad, a halin yanzu yajin cin abinci ya yadu zuwa sauran garuruwa kamar su Lahur,Karaci da sauran su.
Ga hirar da abna ta yi da Gulam hur shubairi daya daga cikin manya maluman.
Abna; tambaya ta farko shin menene asalin fara yajin cin abinci da shaikh Raji Jafari ya shiga?
Gulam ;shekara da shekaru ‘yan ta’adda a kasar Pakistan suke kashe mabiya mazahabar shi’a wanda ya zuwa yau sun kashe sama da mutun 27000 kuma hukumomi a kasar sun sa ido suna kallom ‘yan ta’addar na yawo cikin ‘yan ci wasu ma daga cikin su ana basu kula ta musamman.
A lokaci guda kwamnatin Nawaz sharif na gwacema ‘yan shi’a filayen su kuma ana kama su ba tare da wani dalili ba.
Abna ;kamar ta yane kwamnati ke karbe filayen ‘yan shi’a?
Gulam; garuruwan Gulgut da Baltistan na daya daga cikin yan kunan mabiya mazhabar shi’a amma sojojin kwamnati suna amfani da karfe wajen kwace filayen mazauna yakin domin su raunana su.
Abna; wane irin zalunci ne ake nuna maku?
Gulam ; sojojin kwamnati sun kai hari kan masu gudanar da bukin maulidin Imam Hussain{a.s}a garin yaracina wanda hakan yai sanadiyar shahadar mutane da dama hakama abun yake a garin Dira Isma’il a rana daya sun kasha mutane hudu amma ba abunda hukuma tace.
Abna ; shin kana ganin wannan yajin cin abincin zai Haifa da mai ido?
Gulam :majalisar hadin kan masulmi da Hujjatul islam Raji Abbas sun daura niyar cigaba da yajin cin abinci har sai hukumomi sun biya masu bukatocin su da kuma haka ne duniya zata fahinci halin da ‘yan shi’a suke a Pakistan.
Abna ; menene bukatun masu yajin cin abincin?
Gulam ; suna bukatar abubuwa bakwai ne kamar haka.
1-daukar mataki akan kashe ‘yan shi’a da akeyi a garuruwa daban daban na Pakistan
2-aika fayil din masu laifi zuwa kotun koli ta soja
3-janye dokar hana juyayin shahadar Imam Hussain{a.s}a yankin fanjab
4- hana masu kafirta mulusmi damar aikata aiyukan su
5-daukar matakin da ya dace akan kisan da aka yima ‘yan shi’a a yankin khaibar fakhtunkha
6-hada kwamitin bincike akan kisan da sojoji suka yi ma ‘yan shi’a a yan kin Farcanar
7-mai dama wadanda aka raba da filayen abun su
Masu yajin cin abincin sun sha alwashin idan ba abiya masu wadannan bukatun guda bakwai b aba zasu janje daga aniyar su ba.
Abna ; shin kana ganin hukuma za ta biya maku wadannan bukatu?
Gulam ; labarin yajin cin abincin ya zagaya ko ina acikin kasar Pakistan wanda hakan yasa wasu garuruwa suka shiga cikin sahun masu yajin cin abincin amma abun takaici har yanzu hukumomi basu ce komi aba amma ta bankare guda masu yajin cin abincin sunce ba za suyi kasa a gwiwa ban a cigaba da yajin har sai sun memoma al’ummar su yanci,
Abna ;yau kwana nawa Kenan da fara yajin?
Gulam ;yau kwana sha tara Kenan.
Abna ;mutane nawa ne tare da Hujjatul islam Raji Jafari suke wannan yajin cin abincin?
Gulam ; farko shaikh Raji Abbas ne ya fara amma kuma daga baya dukkanin shuwagabanin majalisar hadin kan musulmi sun bi sahun sa kuma kamar yadda na ambata a baya mutane a sauran garuruwa suma sun shiga cikin jerin masu yajin cin abincin.
Abna ; a ina ne masu yajin cin abincin suka taru?
Gulam ;sun hadune a cibiyar manema labarai dake Islam Abad.
Abna ; ya lafiyar masu yajin cin abinci take?
Gulam ; a bayyane yake cewa suna cikin mawuyacin hali wanda hakan tasa aka kai sheikh Jafari asibiti amma bayan awa biyu ya sake dawowa wurin taron.
Abna ; wane abu kake bukata ka yan shi’a na sassan duniya?
Gulam: bukatata shine su san halin da al’ummar musulmi musamman yan shi’a suke ciki a Pakistan kuma su nuna damuwar su akan hakan.
Abna ; akwai maganar da ta saura?
Gulam ; ina kira ga manyan maluma da maraja;ai da sauran masana akan su taimaka domin gani yan shi’a na Pakistan sun fita hakin da suke ciki.
Abna ;mun gode.288