7 Maris 2016 - 13:24
Gwamnatin Masar Ta Tuhumci Kungiyar Yan Uwa Musulmi Da Hamas A Kisan Babban Mai Gabatar Da Kara Na Kasar

Gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan cewa kungiyar Ikhwanul Muslimin da kuma ta Hamas a yankin Gaza sune ke da hannu a cikin harin da ya kashe babban mai gabatar da karara kasar Hisham Barakat a shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalti Majdi Abdulgaffar ministan cikin gida na kasar Masar yana fadin haka a wani taron yan jarida da ya kira. Ministan ya kara da cewa a halin yansu suna tsare da mutane 6 wadanda ake tuhuma da wannan lamari har zuwa kwanaki 15 don karin bincike a kansu.

Hisham Barakar dan shekara 64 a duniya ya rasu ne bayan da motarsa ta taka nakiyan da aka bisne a kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki a cikin watan yunin shekara ta 2015 da ta gabata.288