3 Agusta 2015 - 07:33
Nijar na bikin cika shekaru 55 da samun ‘yancin kai

Yau 3 ga watan Agusta Jamhuriyar Nijar ke bikin cika shekaru 55 da samun ‘yancin-kai daga turawan mulkin mallakar Faransa, kuma shugaban kasar Mahamadou Issifou ya yi jawabi ga al’umma kan batutuwa da dama.

Muhimman batutuwa uku ne shugaban ya fi mayar da hankali a cikin jawabinsa da suka hada da tsaro, da lattin daminar bana sannan da batun zabubbuka masu zuwa

Amma shugaban bai tabo batun cin hanci da rashawa ba da kuma batun rage farashin man fetir da al’ummar kasar ke bukata.288